1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadain 'yan adawa a Chadi

Salissou BoukariJuly 10, 2016

'Yan adawa a kasar Chadi sun yi kira tare da jan hankalin kasashen duniya kan halin kama karyan da ake fuskanta a gwamnatin Shugaba Idriss Deby Itno.

https://p.dw.com/p/1JMeQ
Tschad Proteste Zivillgesellschaftsorganisationen und Opposition
Hoto: DW/D. Blaise

'Yan adawan na Chadi sun ja hankalin kasashen duniya kan halin da kasar ka iya fadawa sakamakon shiru da suka yi na kin kulawa da halin kama karyan da ake fuskanta daga gwamnatin shugaban kasar Idriss Deby Itno, wanda ke kan karagar mukin kasar tun daga shekara ta 1990. 'Yan adawar dai na zargin Shugaba Deby da yin tazarce ta hanyar nuna karfin iko. Hadin gwiwar jam'iyyu 15 na bangaran 'yan adawar kasar ta Chadi dai sun sanar da wadannan bukatu nasu ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a karshen wani zama da suka yi na yini uku a Ndjamena babban birnin kasar, inda suka yi kira ga al'umma da su kasance cikin shiri na amsa kira nan ba da jimawa ba.