1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi na shirin kirkiro da Jamhuriya ta hudu

Salissou Boukari
March 19, 2018

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya sanar da tsarin kafa Jamhuriyar ta Hudu a kasar. Shugaban ya sanar da wannan batu ne yayin bude wani babban zaman taro don kawo sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/2ubRZ
Tschad Präsident Idriss Deby
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ItnoHoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Shugaba Deby ya yi kira ga mahalarta taron tare da jan kunnensu kan mahimmancin wannan zama ga kasar ta Chadi da al'ummarta baki daya, inda ya ce cikinsa ne za a kirkiro da Jamhuriya ta hudu. Wannan zama ne dai shi ne na farko tun bayan wanda aka yi na kaddamar da kundin tsarin mulkin kasar a shekara ta 1996.

Mahalarta taron fiye da 700 ne za su dukufa cikin su kuwa har da tsohon shugaban kasar ta Chadi Goukouni Weddeye, da shugabannin addinai, da sarakunan gargajiya da mambobin gwamnati, da kuma 'yan kasar ta Chadi da ke a kasashen waje, inda har ya zuwa ranar 27 ga wannan wata na Maris za su fito da sabon kundin tsarin mulki na jamhuriya ta Hudu a kasar ta Chadi. Sai dai 'yan adawar kasar da wani bangare da kungiyoyin fararan hulla sun karwarewa halartar taron.

Gyaran kundin tsarin mulkin kasar ta Chadi, zai bada damar sauya wa'adin mulkin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da ake iya sabuntawa sau daya, sannan da kirkiro majalisar dattawa, da kuma sake karkasa jihohin a kasar. Sai dai 'yan adawan kasar na ganin cewa wani mataki ne na bai wa shuaga Deby damar kara makalewa a kan mulki.