1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta rufe kan iyakar ta da Sudan

April 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1w

A rikicin da ta ke yi da makwabciyar ta Sudan, shugaban Chadi Idris Deby ya katse duk wata hulda ta diplomasiya da gwamnatin birnin Khartoum. Baya ga haka shugaban na Chadi ya ba da umarnin rufe kan iyakar kasar sa da Sudan. Shugaba Deby ya kuma yi barazanar korar ´yan gudun hijirar su kimanin dubu 200 wadanda suka tserewa rikicin lardin Darfur na yammacin Sudan daga Chadi. Shugaba Deby na zargin Sudan da marawa ´yan tawayen da ke kokarin kifar da gwamnatinsa baya. Alkalumman da gwamnatin Chadi ta bayar sun yi nuni da cewa an kashe mutane sama da 500 sakamakon mummunan fadan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawayen da suka yi kokarin hambarad da gwamanti.