1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Charles Taylor ya gurfana gaban kotun duniya a birnin The Hague

July 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bupr

Tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor ya gurfana a karon farko a gaban kotun kasa da kasa dake birnin The Hague na kasar NL a wata shari´a da zata share fagen kararsa da aka yi na aikata laifukan yaki. Tsohon madugun ´yan tawayen dai bai furta komai ba lokacin zaman sauraron shari´ar. Mista Taylor na fuskantar jerin tuhuma har 11 da suka hada da aikata laifukan yaki da cin zarafin ´yan Adam musamman na jagorantar yiwa mutane kisan gilla, fyade da kuma nakasad da dubban mutane a lokacin yakin basasan kasar Saliyo na shekaru 10. Ya ki amsa laifin sa, amma ana iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai har in same shi da aikata wadannan laifuka.