1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Girgizar kasa sau biyu a kasa da sa'o'i 24

August 9, 2017

An samu girgizar kasa sau biyu cikin kasa da kwana guda a kasar China lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai da kuma jikkatar wasu sama da 60,

https://p.dw.com/p/2hueo
China Rettungskräfte suchen nach Verschütteten nach Erdrutsch in Gengdi
Hoto: Reuters

Bayanan da ke fitowa daga arewacin kasar China na cewa an sake samun wata girgizar kasa cikin kasa da sa'o'i 24 lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai da kuma jikkatar wasu sama da 60 a cewar mahukunta. Ibtila'in ya faru ne a larduna Xinjian da Sichuan wadanda ke arewa maso yammacin kasar, kuma ta baya-bayan nan ta faru ne a kusa da kan iyakar kasar da Kazakhstan, a wani wajen da baki 'yan yawon bude ido ke kai wa ziyara.

Wasu rahotannin ma dai sun ce an samu zaftarewar laka da ta rutsa da 'yan yawon bude ido kimanin 100, tare da ragargaza gidaje masu yawan gaske. Akwai kuma alamun yawan wadanda suka mutu ka iya zarta alkaluman farko da mahukunta suka bayyana.

Wannan dai yanki ne da bala'in ya saba faruwa a cikinsa, inda ko a shekara ta 2008 ma sai da sama da mutum dubu 700 suka salwanta.