1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China Taƙi ƙara dajajar kuɗinta

March 14, 2010

Firimiyan ƙasar China ya yi watsi da kiran ƙasashen yamma na ɗaga darajar kuɗin ƙasar

https://p.dw.com/p/MSb4
Firimiyan ƙasar ChinaHoto: AP
Gwamnatin ƙasar China ta yi watsi da matsin lambar ƙasashen yamma na ta ƙara darajar kuɗin ƙasar wato Yen. Da yake jawabi ga taron majalisar al'ummar ƙasar ta China, firimiya Wen Jiabao ya musanta zargin da Amirka da Tarayyar Turai suke yi na cewa, China ta ƙi daga darajar kuɗin ta na Yen domin ta ci gaba da samun haɓaka na kayan da take fitarwa. Tun da farko Kimanin wakilai dubu uku dake hallatar taron majalisar al'ummar ƙasar, suka amince da kasafin kuɗin da shugaban ƙasar Wen Jibao ya gabatar mata. Kasafin na shekara 2010 goma zai cika giɓin da aka samu a sakamakon rikicin tattalin arziki da duniya da shiga. Ƙasar ta China ta tsara yadda za ta ƙara yawan kuɗin da take kashewa domin tallafawa koma bayan da aka samu, ta fannin kayan da take fitarwa. Shugaban Wen Jibao ya kuma yi alƙawarin zai ƙara yawan kayan da kasar ta China ke sayowa daga waje, kuma ya buƙaci sauran ƙasashen duniya su ma su yi hakan. Manufar shugabannin Beijing dai shine asamu haɓakar tattalin arziki da kashi takwas cikin ɗari. Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Ahmad Tijjani Lawal