1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta amsa cewa ´yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zanga

December 11, 2005
https://p.dw.com/p/BvH2
Bayan an shafe kwanaki da dama ba tare da tace uffan ba, yanzu haka dai gwamnatin China ta amsa cewar ´yan sanda sun bude wuta akan wasu mutane dake zanga-zanga a wani kauye dake kudancin kasar. Kamfanin dillancin labarun kasar Xinhua ya rawaito cewar mutane 3 suka rasu sannan wasu 8 suka ji rauni sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zanga a kusa da Shanwei dake lardin Guangdong a ranar talata da ta gabata. Da farko dai wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce akalla mutane 30 ´yan sanda suka bindige har lahira. Su dai masu zanga-zangar na bukatar gwamnati ta biya su diyya ne bayan ta kwace masu filayen don gina wata tashar makamashi.