1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta jaddada Kudiri na inganta muhalli

March 5, 2017

A babban taron shekara na jam'iyya mai mulkin kasa, Firimiyan China Li Keqiang ya ce gwamnati za ta bada kulawa ta musamman wajen tsabftacce iskar muhalli a daura da kalubalen tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/2Yf1I
China CPPCC Chinesische Volkspolitische Beratungskonferenz
Hoto: picture alliance/Photoshot/J. Peng

Firimiyan China Li Keqiang ya ce kasar ta biyu mafi karfrin tattalin arziki a duniya na fuskantar gagarumin kalubale yana mai nuni da raguwar cigaban tattalin arzikin yayin da ya rage hasashen tattalin arzikin kasar a bana zuwa kashi kimanin kashi 6.5 cikin dari.

Dama dai tattalin kasar na tafiyar hawaniya tun cikin shekaru 25 da suka wuce. A shekarar 2016 tattalin arzikin ya tsaya ne a kashi 6.7 cikin dari wanda ke zama mafi rauni tun shekarun 1990.

A waje guda kuma Firimiyan na China yace kasar za ta dauki kwararan matakai na inganta iskar muhalli.

" Ya ce za mu sake mayar da sararin samaniyar mu ya zama shudi ma'ana za mu inganta tsabtar iskar. Hakan nan kuma za mu karfafa binciken kimiya domin kawar da gurbatar muhalli."

Kungiyoyin rajin kare muhalli a China sun yi maraba da sabbin matakan da Firaministan ya bayyana.