1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chirac ya nemi afuwar Turkiya a game da dokar Majalisar dokokin kan Armeniya

October 15, 2006
https://p.dw.com/p/Buft

Shugaban ƙasar Faransa Jacques Chirac ya nemi afuwar P/M Turkiya Tayib Erdowan a game da ƙudirin da yan Majalisun dokokin Faransan suka zartar dake baiyana cewa laifi ne a musanta cewa Turkiya ba ta yiwa Armeniyawa kisan ƙare dangi ba, a zamanin mulkin Othman Turks. Erdowan ya shaidawa yan jamíyar sa cewa shugaba Chirac ya yi magana da shi ta waya yana mai neman afuwa bisa zartar da wannan ƙudiri. Ita dai ƙasar Turkiya ta musanta cewa ta yiwa Armeniyawa kisan ƙare dangi, ta ce ƙaddara ce ta yaƙin siyasa ta faɗawa Armeniyawan amma ba kisan gilla ba. A waje Turkiya ta zargi Armeniya da kisan gilla yayin da ta mara baya ga ƙasar Rasha a mamayen da ta yiwa Turkiya a lokacin yaƙin duniya na daya. Kimanin mutane 100 ne kuma suka gudanar da zanga zanga a ƙofar ofishin jakadancin Faransa a birnin Istanbul domin nuna bacin ran su ga ƙudirin Majalisar dokokin Faransan. Turkawa da dama na ganin batun kisan gisan gillar, wata kafa ce ta hanawa Turkiyan shiga ƙungiyar tarayyar Turai. Hukumar tarayyar Turan ta baiyana cewa yarda da cewa Turkiya ta aikata kisan ƙare dangi a kan Armeniya ba ya daga cikin sharaɗin shiga ƙungiyar EU.