1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da ɓarin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah

August 7, 2006
https://p.dw.com/p/BunU

A na cigaba da ɓarin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah a kudancin Labanon.

Da assabahin yau rundunar tsaron Isra´ila, ta kai sabin hare hare ta sama a kewayen birnin Beyruth, da wasu yankuna na kudancin kasar.

A nata gefe ƙungiyar Hezollah ta bada sanarwar hallaka sojoji 4, na Isra´ila da kuma harba ƙarin rokoki a matsayin martani ga hare haren na Isra´ila.

A fagen diplomatia Majalisar Ɗinkin Dunia ta bayana aniyar ɗaukar wani ƙuduri na kawo ƙarshen wannanrikici, to saidai, ƙasashen larabawa, sunyi wasti da ƙudurin da su ka zarga, da nuna fifiko ga Isra´ila, kamar yada ministan harakokin wajen Syria walid Mouallem ya nunar:

„Wannan tsuman ƙuduri,ƙofa ce ta buɗa ci gaban yaki.

Kuma na 2, ƙofa ce ta yiwar ɓarkewar yaƙin bassasa a Labanon, wanda babu mai buƙatar sa ,sai Isra´ila“

A daya hannun, ministan harakokin wajen Syria, ya ce kasar sa, a shire ta ke, ta yaƙi da Isra´ila.

Nan gaba a yau ne, bisa gayyatar ƙasar Saudia, ministocin harakokin wajen ƙasashen larabawa, za su shirya zaman taro a birnin Beyruth, domin cenza miyau a kann hanyoyoj warware wannan rikici.