1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaba da dambaruwar siyasa a Libanon

November 23, 2007
https://p.dw.com/p/CSCC

A yau wa´adin da aka bawa wakilan majalisar dokokin Libanon na zaban sabon shugaban ƙasa ya ke ƙarewa. To amma har yanzu an kasa samun wata masalaha tsakanin jam´iyun da ba sa ga maciji da juna duk da matsin lamba daga ƙasashen duniya. Yanzu haka dai an dage wani zaman karshe a ƙoƙarin da ake yi na zaɓen mutumin da zai maye gurbin shugaba Emile Lahoud. Yanzu haka dai ministocin harkokin wajen ƙasashen Faransa, Italiya da kuma Spain sun nuna shakkun cimma wani tudun dafawa bayan sun yi kai gauro suna kai mari da nufin cimma wani daidaito a kan dan takara guda ɗaya. A kuma halin da ake ciki ´yan adawan Libanon karkashin jagorancin kungiyar Hisbollah sun ce zasu ƙauracewa zaman majalisar dokokin a yau juma´a. A ƙarƙashin tsarin mulkin kasa, idan ba a zabi wani ɗan takara da zai maye gurbin shugaba Lahoud ba, to za a miƙa ikon sa ga gwamnati.