1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da fada a Somalia

Hauwa Abubakar AjejeMay 12, 2006

An shiga kwana na 6 na tashe tashen hankula tsakanin kungiyar yan tawaye da magoya bayan malaman islama a babban birnin kasar Somalia,Mogadishu,inda yanzu haka akalla mutane 130 suka rasa rayukansu

https://p.dw.com/p/Bu09
Hoto: AP

Yan kungiyoyin islama dana yan tawaye suna ci gaba da kokarin kame babban birnin kasar ta Somalia,Mogadishu.

Bangaren kotunan musuluncin sunce,wasu Karin mutane 5 sun rasa rayukansu cikin fada na daren jiya,yayinda fadan ke kara bazuwa daga yankin Sisi dake babban birnin kasar zuwa lardin Yaqshid.

Kakakin kungiyar yan tawaye,Hussein Gutale Rage,yace yanzu haka wadanda aka kashe sun kai mutum 150,sai dai babu tabbacin hakan.

Daruruwan mutane dai sun samu rauni cikin fada daya barke tun ranar lahadi,mafi yawansu sakamakon harbe harbe da bindigogin atilare,da kuma albarusai akan gidajen farar hula,suna masu kashe mata da yara kanana.

Fadan na wannan mako shine fada karo na uku,cikin wannan shekara tsakanin yan bindiga da suke goyon bayan kotunan islama da kuma kungiyar yan tawaye da take ikararin yaki da taaddanci.

Siyad Muhammad,shugaban bangaren masu dauke da makamai na kungiyar islama,ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,da wuya a iya kirga yawan wadanda suka halaka,amma kuma yawansu sai karuwa yakeyi,ya kuma tabbatr da ci gaba da fada a lardin Yaqshid.

Akalla kashi 70 cikin dari na mazauna lardin sun tsere daga gidajensu sakamakon fadan na baya bayan nan.

Kakakin nay an tawayen yace,zasu ci gaba da fada muddin dai bangaren islama na ci gaba da ja dasu.

Wannan fada kuwa na kara ci gaba,duk da kiraye kirayen a kwantar da hankula da kasashen duniya sukeyi,wanda tuni gwamnatin rikon kwarya mai rauni na kasar tayi,wadda yanzu haka take da zama a garin Baidoa yammacin birnin Mogadishu.

Amma kungiyar yan tawaye ta ARPCT tayi watsi da wadannan kiraye kiraye da kuma tayin zaman lafiya da kungiyar islaman ta mata,inda yanzu haka tashe tashen hankula suka fi karfin rikicin kwanaki 3 da akayi a watan fabrairu da kuma na kwanaki 4 a watan maris,inda akalla mutane 85 suka rasa rayukansu.

Wadannan tashe tashen hankula sune mafiya muni tun rushewar gwamnatin Somalia shekaru 15 da suka shige.

Yan tawayen dai sun lashi takobin rage karfin shugabannin islama,wadanda suka samu goyon baya matuka saboda samarda dan kwanciyar hankali a wasu bangarori na Mogadishu,ta hanyar bullo da dokokin shariar muslunci.

Kungiyar ta yan tawaye ta kuma zargi shugabannin islaman da laifin boye yan taadda da kuma horasda masu jihadi daga kasashen ketare,zargi da Amurka da wasu kasashen yamma suka yarda da shi.

Kodayake Amurkan bata fito fili ta goyi bayan kungiyar yan tawayen ba,amma jamian kungiyar sun fadawa kanfanin dillancin labari na AFP cewa,kungiyar ta karbi taimakon kudi daga Amurka kuma suna aiki tare wajen kare yaduwar tsatsauran raayi na islama.