1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da rikici a kudancin Kamaru

Usman Shehu Usman
February 1, 2017

Hukumomi na ci gaba da daukar tsatsaurar matakan dakile yunkurin da gungun kungiyoyi ke yi na  kara fadakar da jama'a a game da fafutukar ballewa da al 'ummar kasar masu magana da harshen Turancin Inglishi ke yi.

https://p.dw.com/p/2WoIa
Shugaban Kamaru  Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya Hoto: imago/Xinhua Afrika

Gwamnatin na yin amfani da lamarin na yankunan arewa maso yammci na Bemanenda da kuma kudu maso yamamaci na Buea wanda ke naman ballewa daga Kamarun,domin saka takunkumi ga 'yan jarida, tare da tsinke hanyoyin sadarwa na yanar gizo a wasu yankunan.Lamari na baya-baya nan shi ne matakin da hukamar tace labarun kasar ta CNC ta dauka na haramta wasu gidajen radiyon da talabijan wadanda za su rika yada bayyanai na masu da'war warewa daga kasar.Tchounkeu Severin shi ne shugaban gidan talabijan na Equinoxe.

"Ya ce''Mun sha fama shekara da shekaru domin samun yancin fadar albarkacin baki, da kuma na soke saka takunkumi.To amma a yanzu hukumar CNC na ba da dama ga gwamnatin na mayar da mu baya ta hanyar take yancin 'yan jarida ba za ta sabu ba.''

Matakin gwamnatin dai na Kamaru bai tsaya ba kawai ga kafofin yada labarai na cikin gida ba har ma da wakilan gidajen rediyo na waje irinsu Detsche Welle masu wakilai a yankin kudancin kasar inda ake yin magana da harshen turancin Inglishi, sakamakon yadda aka yi wa wakiln na DW barazana. Peter Nkanga na daya daga cikin shugabannin kungiyoyin masu fafutukar kare yancin 'yan jarida a yankin yammai Afirka.

Ya ce ''Gwamnati dole ne ta daina yin wannan irin barazana ga kafofin yada labarai, abin da yakamata ta ya yi shi ne na tattaunwa da 'yan jaridan domin samun mafita a rikicin.''

Tun a cikin watan Nuwamba da ya gabata ne al'ummomin yankunan na kudancin Kamaru wadanda ke zaman kishi 20 cikin dari na yawan al'ummar kasar miliyan 22 ke yin zanga-zanga domin neman yancin gashin kai. Sai dai kuma gwamnatin ta dage cewar ba za a iya raba kasar biyu ba.