1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da sauraron shari´´ar Saddam Hussain

December 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvFT

Tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussain ya karyata bayanin daya fito daga fadar White House ta Amurka, cewa karya yake , babu wani dandana kudar sa da yayi, a lokacin yana tsare a hannun sojin Amurka a Bagadaza.

Saddam ya fadi hakan ne kuwa a lokacin da yake jawabin a gaban kotun dake tuhumar sa tare da mukarraban sa guda 7, a Bagadaza aci gaba da zaman kotun karo na bakwai.

A jiya ne dai Tsohon shugaban kasar ta Iraqi ya shaidawa kotun cewa ya sha duka a hannun sojin Amurka a lokacin yana hannun su, wanda ba tare da bata lokaci ba Fadar ta White House ta karyata wannan batu da cewa hankali ba zai yarda dashi ba.

Ya zuwa yanzu dai tuni alkalin kotun ya bayar da umarnin gudanar da wadan nan korafe korafe na Saddam Hussain nin.

A waje daya kuma a yau alhamis masu bada shaidu game da tuhumar da akewa Saddam Hussain da mukararraban nasa 7 naci gaba da bayar da bayani game da kisan kiyashi daya faru a garin Dujail a shekara ta 1982.

Matukar dai aka samu Saddam da mutanen sa da aikata wannan laifi na kisan kiyashin to babu shakka hukuncin kisa ya hau kansu