1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da shari´ar Saddam Hussain a yau

February 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6b

A yau ne ake ci gaba da sauraron shari´ar da akewa tsohon shugaban kasar Iraqi, wato Saddam Hussain tare da mukararraban sa guda bakwai a birnin Bagadaza.

Kotun zata ci gaba da zaman ta ne yau, bayan dage saurarron karar da alkali Abdel Rahmanan yayi na tsawon makonni biyu.

Mahukuntan kasar na Iraqi dai na zargin Saddam da mukararraban nasa ne da kisan kiyashi na mutane sama da dari a garin Dujail a shekara ta 1982.

Babban lauyan dake kare Saddam Hussain , wato Khalil al Dhulaimi yace a shirye suke su fara halartar zaman wannan kotu.

Idan dai za a iya tunawa tawagar dake kare tsohon shugaban kasar ta daina halartar zaman kotun ne , bisa abin da ta kira rashin adalci da gaskiya a game da yadda ake gudanar da sauraron shari´ar.

A waje daya kuma, bayanai sun nunar da cewa Saddam Hussain ya kawo karshen yajin aikin kin cin abinci daya fara a watan daya gabata, don nuna bacin ransa a game da yadda shari´ar tasa take gudana.

Bayanai dai sun nunar da cewa, da alama daukar wannan mataki na Saddam nada nasaba da lafiyar sa ne.