1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaba da tashe tashen hankula a yankunan Falasdinawa

May 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuxV

´Yan bindigar Falasdinawa sun farma harabar ginin majalisar dokoki dake birnin Ramallah don nuna fushinsu game da raunin da shugaban hukumar leken asiri ya samu a Zirin Gaza. ´Ya´yan kungiyar baradan Al-Aqsa dake daukar makami na kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas sun shiga wurin da ake ajiye motoci dake cikin harabar majalisar inda suka yi harbi cikin iska. Hakan ya faru ne sa´o´i da dama bayan shugaban hukumar leken asiri Falasdinu Tareq Abu Rajb ya samu mummunan rauni sakamakon fashewar bam a harabar ginin hukumar dake birnin Gaza. ´Yan bindigar Al-Aqsa sun zargi kungiyar Hamas ta masu kishin Islama da hannu a fashewar bam din. Hakan kuwa ya faru ne a daidai lokacin da ake samun hauhawar tsamari tsakanin dakarun tsaron Falasdinawa masu biyayya ga shugaba Mahmud Abbas da kuma masu goyawa kungiyar Hamas baya. A kuma halin da ake ciki, a karon farko sojojin sa kai na Hamas sun fadada yawan su a Zirin Gaza inda suka mamaye wurare a bangaren Falassdinu na kan iyakar su da Masar.