1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tashe-tashen hankulla a kasar Iraki

February 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8z

A ci gaba da tashe tashen hankullan a kasar Iraki mutane fiye da 10 ne, su ka rasa rayuka a sahiyar yau talata.

Sojojin Amurika 4 sun gamu da jalinsu, a yayyin da wata nakiya ta fashe a birnin al Anbar, dake yammancin kasar.

A baki daya, jimmilar sojojin Amurika 2.225 kenan, su ka mutu a cikin yakin na kasar Iraki, daga farkon shi a shekara, ta 2003 zuwa yau.

Shima magajin garin Birnin Fallujah, Cheik Kamal Chaker Nazal,ya rasa ransa a yau talata, bayan da wasu mutane da ba a tantance ba,su ka fesa mashi luggudan wuta.

A hannu daya kuma, kurrarun massana na hukumar kiwon lahia, ta Majalisar dinkin Dunia,sun fara aiki a kasar Irakin, domin binciko haske, a game da cutar murra tsintsaye, da ta hadassa mutuwar mutane 2, a wannan kasa.