1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tattaunawa tsakanin Uganda da yan tawayen LRA

July 18, 2006
https://p.dw.com/p/BuqA

A yau masu shiga tsakani na Uganda da wakilan kungiyar LRA zasu ci gaba da tattauna batun tsagaita bude wuta a kokarinsu na kawo karshen yakin basasa mafi tsawo a nahiyar Afrika.

Masu shiga tsakani daga kudancin Sudan sun zabi wasu batutuwa 5 daga cikin bukatun da bangarorin 2 suka mika a tattaunawarsu ta ranar lahadi,wadanda suma zasu tattauna akansu.

Mataimakin shuganan kudancin Sudan Riek Machar da kuma wakilan gwamnatin Uganda sun bukaci shugaban kungiyar LRA Joseph Kony ko mataimakinsa dayansu ya halarci wannan tattaunawa,

sai dai dukkaninsu kotun kasa da kasa dake sauraron laifukan yaki tana nemansu ruwa a jallo,inda yanzu haka suke boye cikin dazuzzukan arawa maso gabashin Kongo.

Magoya bayansu dai an sansu da kashe farar hula ko kuma yanke masu gabbansu,tare da sace yara kusan 20,000.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni a halin da ake ciki,yace tilas ya mikawa shugaban LRA tayin ahuwa,duk kuwa da nemansa da kotun kasa da kasa takeyi,saboda a cewarsa babu wata kasa a yankin da zasu dogara a kanta wajen cafke shugabbanin LRA.