1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da ziyarar Rice a Jamus

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuUB

Nan da yan saoi kadan ne sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice zata gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ci gaba da ziyararta zuwa Jamus,bayan rangadinta na yankin gabas ta tsakiya.

Rice da takawaranta na jamus Frank Walter Steinmeier sun sanarda cewa jamian wakilan kasa da kasa 4 dake tatauna batun zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya zasu gana nan gaba cikin watan fabrairu mai kamawa.

Wakilan sun hada da na majalisar dinkin duniyaAmurka,Rasha da kungiyar taraiyar turai.

Bayan tattaunawar tasu a birnin Berlin Steinmeier yace akwai bukatar gagauta sasanta matsalar gabas ta tsakiya.

Rice da Steinmeier sun kuma tattauna batun nukiliya na Iran,inda Rice din ta sake nanata matsayin Amurka gem da tattauna harkokin hulda da Iran har sai ta dakatar da inganta sinadarenta na uraniyum.