1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban ɓarin wuta a Somalia

April 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuN2

A ƙasar Somalia, ana ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun gwamnati, masu goyan bayan Ethiopia, da kuma na kotunan Islama.

Yau kwana na 7 kenan, da ɓangarorin 2 ke gwabzawa, da manyan makamai.

Gwamnatin ta alƙawarta cewar dakarun ta za su ci gaba da fafatawa, har sai sun kakkaɓe yan yaƙin sunƙuru daga ƙasar Somalia.

A cewar ƙungiyoyin masu zaman kan su, ya zuwa yanzu, a ƙalla mutane 30 su ka rasa rayuka, a tsukin kwanaki 7 da su ka gabata.

Sannan kussan mutane rabi milion su ka shiga halin gudun jihira.

A sahiyar yau, faɗan ya ƙara tsamari, bayan da sojojin gwamnati, su ka yi luggudan wuta, ga yankunan yan yaƙin sunƙurun.

Wannan shine bala´i mafi muni, da ƙasar Somalia tun bayan kiffar da shugaba Mohamed Siad Bare, a shekara ta 1991.