1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban kone konen motoci a Faransa

November 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvKs

A kasar Fransa, masu zanga zanga na unwaganin ya ku bayi na cigaba da kone konen motoci.

A dare na 20, da fara wannan zanga zanga sun kone motoci 163 da kadarori masu yawa, a yayin da jami´an tsaro su ka capke mutane 71.

A jimilce daga fara wannan tashe tashen hankulla ranar 27 ga watan oktober, ya zuwa yanzu, motoci 9.000 su ka kone, sai kuma mutane 2.888 da ke hannun jami´an tsaro.

Tunni, Kotu ta yanke wa wasu, daga cikin su hukuncin dauri.

A yammacin jiya yan majalisar dokoki sun kada kuri´ar amincewa da tsawaita dokar hana yawan dare, a unguwaninda rikicin ýa fi kamari, har tsawan wattani 3 masu zuwa.

Ministan kula da kaywattata rayuawar iyali ,da ta ke bayyani a kan wannan rigingimu, ta nunar da cewa aure auren mata barkatai, da cunkusso, a unguwanin baki yan ci rani na Fransa, su ne tushen barkewar wannan rikici.