1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban rangadin kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai a yankin Gabas ta Tsakiya

March 18, 2010

Kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai kan manufofin Ƙetare na ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/MW1e
Catherine Ashton tare da Avigdor Liebermann, ministan harkokin wajen Isra'ilaHoto: AP

Kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ƙetare, ta isa birnin Gaza domin shiga tattaunawa tare da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma gano yadda ake amfani da kuɗaɗen taimako da Ƙungiyar Tarayyar Turai ke bai wa wannan yanki da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas. Catherine Ashton, ta kai wannan ziyara ne a matsayin yanki na rangadin yini biyar da ta ke yi a yankin Gabas Ta Tsakiya inda tuni ta ya da zango a Masar, Syria, Libanon Jordan, Isra'ila da kuma Gaɓar yamma da Ƙogin Jordan. A gobe juma'a idan Allah ya kaimu Ashton za ta zarce zuwa birnin Moscow domin halartan taron rukunin nan na Kawatet da zai duba hanyoyin komawa ga tafarkin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falisɗinawa. Da safiyar yau ne Ashton ta kammala ziyara a Israila inda ta tattauna tare da da Shugaba Shimon Peres. Peres ya ce Isra'ila tana nazarin tsarin da ya dace domin komawa ga teburin tattaunawa tare da Falisɗinawa.

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala