1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban rikici a kasar Habasha

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMp

A birnin Addis Ababa na kasar Habasha, a na ci gaba da arangama, tsakanin Jami´an tsaro da magoya bayan jam´iyun adawa.

Minikstabn harakokin cikin gada na kasar ya bayana cewa, a yau dan sanda daya, ya rasa ransa kuma 54 sun ji raunuka, a cikin wannan arangama.

Kafanin dullanci labaran Fransa na AFP, ya ruwaito cewa, a bangaren masu zanga zangar mutane 27 jami´an tsaro su ka bindige har lahira tare da raunanna, 150 .

A sakamakon rikicin jiya talata,yan zanga zanga 8 su ka kwanta dama.

Rikicin ya barke a kasar, Habasha, bayan da shuwagabanin jami´yun adawa su ka gayyaci magoya bayan su su fito a titina domin, kin amincewa da sakamakon zaben yan majalisun dokoki na watan Mayu da ya wuce wanda su ka ce akwai babban magudi a cikin sa.

Ya zuwa yanzu jami´an tsaro sunce kura ta lafa kuma sun capke da dama daga masu zanga zangar.