1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

191110 Piratenprozess Hamburg

November 22, 2010

Yau ne ake ci gaba da sauraron shari'ar 'yan fashin jiragen ruwan Somaliya a birinin Hamburg na Tarayyar Jamus.

https://p.dw.com/p/QFV4
Wasu daga cikin 'yan fashin jiragen ruwan da ake tuhuma a Jamus.Hoto: dapd

A birnin Hamburg da ke ƙasar Jamus a yau ne 'yan Somaliya da ake zargi da fashin jiragen ruwa za su bayyana a gaban kotu. Waɗannan Somaliyawa goma, sojojin ƙasar Holland ne suka cafke su, bayan da suka yi fashin jirgin ruwan ƙasar Jamus a gaɓar tekun ƙasar ta Somaliya. Wannan dai shi ne karo na Farko a ƙasar ta Jamus da za a yi shari'a kan fashin a teku cikin shekaru 400.

A birnin na Hamburg dai tun shekaru aru-aru da suka gabata an yanke hukunci kan masu fashin a teku kimanin 500. Kuma a wancan lokacin a kan yanke hukuncin cikin sauri, walau dai na ɗauri a gidan yari ko kuma na fille musu kawuna.

Duk da cewa an yi shekaru ba a zartar da irin wannan hukunci ba, amma har yanzu alƙalai na iya samun wata dafara da zas u yanke hukunci walau na cin tara ko ɗauri. Kasancewa an yi fashin jirgin ruwan Jamus da ke ɗauke da kwantenoni, za a iya amfani da dokar aikata manyan laifuka ta ƙasar Jamus. An dai kawo Somaliyawan birnin Hamurg ne ƙarƙashin yarjejeniyar dokokin ƙasa da ƙasa na aikata laifi kan teku- dokar da ƙasar Jamus ta sanya wa hannu. Farfesa Uwe Jenisch masanin dokar kan teku ne da ke jami'ar Kiel a arewacin Jamus. Ya ce:

"Fashi kan teku abu ne da za a iya yanke hukunci akai a dokar Jamus. Kuma dokar ta tanadi ɗauri shekaru biyar a gidan yari. Idan kuma a yayin fashin an samu mutuwa, to hukuncin ba zai gaza shekaru goma ba. Idan kuma anyi wa mutane fashi, to anan ma dai hukunci kusan ɗaya ne"

Waɗanda da ake zargin dai na iya fiskantar ɗauri na shekaru 15. Amma fa sai dai in an yi amfani da dokar ƙasar Jamus kan aikata laifi sace ababen sufuri na ruwa, ciki har da fashin teku. Amma ga dokar ƙasa da ƙasa akwai bambanci kamar yadda Farfesa Jenisch ya bayyana:

"A ƙasashen Denmark da Kanada fashin babu wata doka a kai"

Yanzu dai hukuncin da za a yanke kan masu fashin teku na Somaliyan, abu ne da za riƙa yin amfni da shi kan ƙasar ta Somaliya. Max Johns wakili ne na ƙungiyar lauwoyin kare haƙƙin teku na ƙasa da ƙasa da ke a ƙasar Jamus. Ya ce:

"Akwai masu magana da ke cewa, akasarin Somaliyawa, sun samu kansu ne a wata rayuwa ta tsaka mai wuya. Don haka idan ma aka yanke musu hukunci ɗauri, to hakan ya yi musu a maimakon maida su ƙasarsu da babu rayuwa mai daɗi"

Hukuncin kotu dai koma a wace kotun duniya ba zai kawo wani sauyi ba a ganin mutane irin Muhammed Garani Kadham, wanda ke lura da batun 'yan fashin tekun Somaliya.

"Yaƙi da masu fashin teku ba zai sauya komai ba. Idan ana son yanke kan maciji to da farko sai an warware matsalar ƙasar ta Somaliya"

A shekarun takwas da suka gabata 'yan fashin jiragen ruwa a gaɓar tekun Somaliya sun samu kuɗaɗe masu yawa wajen fansar jirage.

Mawallafi: Wolfgang Dick/Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas