1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban shari´ar tsofan shugaban ƙasdar Irak Saddam Hussain

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2x

A birnin Bagadaza na ƙasar Iraki an koma sauran shari´ar tsofan shugaban kasa, Saddam Hussain.

A zaman na yau, kamar na kwanakin da su ka gabata, an sha masanyar kalamomi zazzafa, tsakanin babban alƙalin kotun da tsofan shugaban ƙasar, bayan da ,

Saddam Hussain,ya ƙi amincewa ya sa hannu, domin a gwada sa hannun sa, da wanda ke kan, wasu takardu na bada umurnin aikata kissa, ga mutane 140, na garin Dujail, lahanin da kotu, ke tuhumar sa, da aikatawa.

Saddam Hussain, ya zargi ministan cikkin gidan Iraki na yanzu, da aikata kisan gilla, ga ɗimbin jama´a, a wannan ƙasa.

A wannan zaman shari´a, tsoffan shugaban, ya gurfana shi kaɗai, ba tare da, sauran mutanen 7 ba, da ake tuhumar su tare.

Tun ranar 19 ga watan oktober ne, a ka fara shari´ar tsofan shugaban kasar Iraki.

Bayan batun kissan kiyassu ga mutane 140, na Dujail, alƙƙallan kotun, sun bayyana wata sabuwar tuhuma, da ke zargin Saddan Husain, da hallaka, a ƙalla ƙurdawa, dubu 100, da kuma yin kaca-kaca, da garuruwa 3000.

Shugaban ƙasar Iraki mai ci yanzu, Jallal Talabani, ya bayyana burin sa, na kotu ta gudanar da shari´a, a kan dukkan wannan lefika, kuma daga ƙarshe, ta yanke hukuncin kissa, ga Sadam Hussain.