1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban taimakon gaggawa zuwa ga al´ummomin Indonesia

May 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuwS

Ƙasashen da ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, na ci gaba da kai taimako zuwa Indonesia,a sakamakon bila´in girgiza ƙasa, da ya abku jiya asabar.

Wannan sabuwar masifa, da ta wakana a tsibirin Java, da ke kudancin ƙasar, ya hadasa mutuwar mutane fiye da dubu 3, sannan fiye da 10. 000 su ka ji mumuman raunuka, inji mataimakin shugaban ƙasar Yusuf kalla.

Ya ce a halin da ake ciki, jami´an kulla da agaji, na fuskantar karancin kayan aiki, duk da taimakon gaggawa da ƙasashen dunia ke ci gaba da kaiwa.

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta bakin sakatare Jannar Koffi Annan, ta ambata kai taimakon magani, da abinci.

Kazalika, ta alkawarta runfuna, ga mutane fiye da dubu 20, da su ka rasa matsugunai.

A nata ɓangare ƙasar Amurika, ta ware taimakon dalla million 2 da rabi.

Sai kuma China, da ta sanar cewa, zata kai dalla million 2, gami da kayan massarufi, ga wanda haɗarin ya rutsa da su.