1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban taron Syrte a game da rikicin Darfur

October 29, 2007
https://p.dw.com/p/C15Q

Ƙungiyoyin tawayen da su ka halarci taron sulhunta rikicin Darfur a birbin Syrte na ƙasar Lybia, sun shawarci ɗage wannan taro, dalilin rashin halartar da dama daga ƙungiyoyin da ke da hannu a cikin wannan rikici.

A wata sanarwar haɗin gwiwar da su ka hiddo, sun gayyaci takwarorin su, da su ka ƙi amsa kira, su lashe amen su, idan kuma ba a cimma wannan buri ba,ƙungiyoyin tawayen sun ce, ɗage taron shine ya fi zama alheri, tare da gayyatar masu shiga tsakani su ci gaba da tuntuɓar ƙungiyoyin da su ka ƙaurace masa, da zumar tsaida wata sabuwar rana, ta koma wa tebrin shawara.

Saidai ƙungiyar taraya Afrika, da Majalisar Ɗinkin Dunia da su ka tsara taron, su nuna rashin amincewa da wannan ɗaukar matakai.

A cewar masu shiga tsakanin, ya fi zama wajibji a ciki gaba da tantanawar birnin Syrte, sannan a ɗaya hannun a ci gaba da lallashin wanda su ka ƙaurace da su cenza tunani.

A baki ɗaya, ƙungiyoyin tawaye 8 su ka ƙi amsa kiran birnin Syrte .