1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya

Ibrahim saniNovember 16, 2005

An bude sabon babin wanzuwar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da yankin Palasdinawa

https://p.dw.com/p/BvUO
Hoto: AP

Bisa wannan yarjejeniya da aka cimma da da yawa daga cikin masu nazarin harkokin siyasa ke kallon ta a matsayin kafa ta bude sabon babin wanzuwar zaman lafiya a yankin,ya zuwa yanzu dai tuni mahukuntan India suka bukaci kasar ta Israela da yankin na Palasdinawa dasu yi aiki tukuru don aiwatar da wannan yarjejeniya yadda ya kamata.

Yin hakan a cewar mahukuntan na India shi zai bada kafar cimma burin da aka sa a gaba na wanzuwar zaman lafiya a yankin na gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin kasar ta Israela da kuma yankin na Palasdinawa.

Bugu da kari mahukuntan na India sun kuma cirawa Faraminista Arial Sharon tuta game da namijin kokarin da yayi na janye dakarun sojin su daga yankin na Gaza, don bawa Palasdinawa damar walwalawa yadda yakamata.

Idan dai za a iya tunawa wannan yarjejeniya ta bude iyakar ta Gaza, an samu cimma ma tane bayan gudanar da wani taron koli a tsakanin Faraminista Sharon da Shugaba Mahmud Abbas da kuma mai shiga tsakani wato sakatariyyar harkokin wajen Amurka CR.

Jim kadan da kammala wannan taro,kafafen yada labaru sun rawaito Rice na fadin cewa nan da kwanako goma za a bude wannan iyaka ta Rafah dake yankin Gaza, wacce tayi iyaka da kasar Masar, don ci gaba da shigi da fici kamar yadda hakan yake ada.

A daya hannun kuma kungiyyar Tarayyar Turai wato Eu cewa tayi a shirye take ta bayar da gudunmawa game da yadda za a aiwatar da wannan yarjejeniya da aka cimma akan bude iyakar ta Gaza. Ya zuwa yanzu ma dai tuni kungiyyar ta Eu ta zabi wani janar din kasar Italiya mai suna, Petro Postolese don zama shugaban tawagar da zasu tabbatar da sauke nauyin da kungiyyar ta Eu ta dauka.

A waje daya shima shugaban yankin Palasdinawa, wato Mahmud Abbas bayyana farin cikin sa yayi da wannan yarjejeniya,domin kuwa ko ba komai zata taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin yankin ta hanyar shigi da ficin kaya a tsakanin yankin da sauran kasashe na duniya.

Duk da wannan yarjejeniya dai da aka cimma, Faraminista Sharon yaki yaci gaba da tattaunawar sulhu da mahukuntan na yankin Palasdinawa.Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan ire hare haren kunar bakin wake ne da masu tsattsauran raayi na yankin keyi ne, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma a tsakanin kasar ta Israela da kuma yankin na Palasdinawa.

Shi kuwa Ministan harkokin Israela wato Silvan Shalon bayyana bacin ransa yayi ga shugaba Mahmud Abbas game da barin kungiyyar nan ta Hamas da za ayi ta shiga takarar zaben da aka shirya yi na yan majalisun dokoki a yankin a watan janairun sabuwar shekara.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan bayani na Shalom ba zai rasa nasaba da zargi ko kuma kallon kungiyyar yan ta´adda da sukewa yan kungiyyar ta Hamas ba.