1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban zanga-zanga a Hongrie

September 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buie

A ƙalla mutane dubu 7 su ka yi kwanan zaune a birnin Budapest na ƙasar Hongrie.

Wannan shine a dare na 4, da a´ummomin ƙasar su ka share a yunƙurin cilastwa Praminista, Ferenc Gyurksany yayi muraɓus daga mukanin sa.

Sadai rahotani daga birnin sun ce jama´a, ba ta zo da yawa ba, kamar sauran kwanaki 3, da su ka gabata, sannan ba a samu ba, yawan tashe -tashen hankula.

Jam´iyun adawa sunyi wasti da kliran kiran gwamnati na hawa tebrin shawarwari.

Saidai sun bada haɗin kai, wajen samun lafawar zanga-zangar, dalilin da ɗage taron gangamin da su ka shirya gudanarwa, ranar assabar mai zuwa,

Shugabanin jam´iyun adawa, sun bayana ɗaukar wannan mataki, domin maido da kwanciyar hankali, kamin zaɓen yan majalisun dokoki da aza a shirya, ranar 1 ga watan oktober mai zuwa.

Wannan zanga zanga, ta samo assali daga watsa wata K7, da redion ƙasa ta yi, inda a cikin kalamomin Praministan da a ka ɗauka ba tare da ya sani ba, ya nunar da cewa ƙarya ce ya shirgawa jama´a, a lokacin yaƙin neman zaɓe , a game da alƙawuran da ya ɗauka, da kuma ayyukan da za shi gudanar, bayan an sake zaɓen sa.