1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban zanga-zanga a Myanmar

September 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuAI

Jami´an gwamnati a birnin Rangoun na Myanmar, sun kiri jama´ar ƙasa su dasa aya ga zanga-zangar da su ke shiryawa.

Rahottani sun nunar da cewa, jami´an sun yi shelar cewa gwamanti, a shirye ta ke, ta ɗauki matakan da su ka dace ,daidai da dokokin ƙasa domin ladabtar da wanda su ka yi watsi da wannan umurni.

Kazalika sun buƙaci supayen ƙasar sun tsame hannuwan su kwata-kwata, daga harakokin siyasa.

A ranar jiya, an gudanar da wata gagaramar zanga-zanga bisa gayyata supayen, wada a karo na farko, a tarihin wannan ƙasa ta haɗa mutane a ƙalla dubu 100.

Daga ƙasashe daban-daban na dunia, an fara matsa lamba, ga sojojin da ke riƙe da ragamar mulki, su saurai koke-koken jama´a.

Ita kanta ƙasar Sin da ke bada haɗin kai, ga gwamatin sojojin Myanmar ta bayana irin wannan buƙata.