1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban zanga-zanga a Thailand

April 5, 2010

'Yan adawa a Thailand na ci gaba da zanga-zanga

https://p.dw.com/p/MnT1
'Yan zanga-zangar nuna adawa da gwamnati.Hoto: AP

A kasar Thailand, masu nuna adawa da gwamnati sun faɗaɗa zanga-zangarsu a babban birnin ƙasar bayan da suka yi watsi da umarnin da 'yan sanda suka ba su da cewa su kawo ƙarshen mamayar da suka yi wa cibiyar kasuwancin ƙasar. A zanga-zangar tasu ta yau Litinin sun mai da hankali ne kan hukumar zaɓe saye da jajayen riguna suna masu barazanar yi wa ginin hukumar ƙawanya har sai shugabanta ya gana da su. Masu zanga-zangar dai su lashi takobin yin matsin lamba har sai gwamnatin Fraministan Abhisit Vejjajiva ta yi murabus domin ba da damar gudanar da sabon zaɓe na majalisar dokoki. Jatupom Prompan, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar ya yi wa babban bankin ƙasar da kuma kamfanin Charoen Pokphand gargaɗi da cewa kada su kuskura su ba da goyon bayansu ga gwamnati.

Mwallafiya: Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu