1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290908 Dialog Wertvolle Schriften

Gineiger, UlrichOctober 23, 2008

A cikin shekarar 1927 aka kafa cibiyar tara bayanai da adana kayan tarihi a birnin Berlin da nufin ciyar da tuntuɓar juna tsakanin addinai daban daban gaba.

https://p.dw.com/p/FfKI
Ministan cikin gida Schäuble da Bekir Alboga a taron Musulunci a BerlinHoto: AP

A bara yawan musulmi a tarayyar Jamus ya ƙaru ya zuwa miliyan 3.5. Daga cikinsu sama da dubu 700 na cikin ƙungiyoyi waɗanda ke ƙarƙashin wakilicin manyan ƙungiyoyin musulmi. An samu waɗannan alƙalumma ne daga cibiyar tara bayanai da adana kayakin tarihi na addinin musulunci a mai mazauni a Soest dake nan Jamus. Daga lokaci zuwa lokaci wannan cibiya na gudanar da binciken jin ra´ayi tsakanin al´ummar musulmi a nan Jamus. Tun a ƙarshen shekarun 1920 aka kafa wannan cibiya a birnin Berlin kuma ta na duba rayuwar musulmi a Jamus wadda ta fara tun a shekara ta 1739. Shirin na wannan karon ya kai ziyara ne a cibiyar tare da tattaunawa da shugabanta.

Salim Abdullah babban daraktan cibiyar tara bayanai da adana kayakin tarihi na addinin musulunci na alfahari da ɗinbim kayakin tarihi da suka haɗa da takardu, littattafai da ƙasidu da cibiyoyin addinin kirista suka buga dake mayar da hankali kan addinin musulunci.

“Duba a nan, ga irinsu nan. Ta haka muke gane irin tunanin wasu game da mu. Ba za mu so nan gaba a riƙa ɓaɓatu kan abin da muka rubuta ba.”

Salim Abdullah mai shekaru 70 yana zaune a cikin wani gida dake wata unguwa a garin Soest wanda aka cika shi da kayakin tarihi daga ƙasa har sama. Wannan gidan shi ne kuma mazaunin cibiyar tara bayanai da adana kayakin tarihin na musulmi a Jamus. Salim mai riƙe da takardun shaidar zama ɗan ƙasashen Jamus da Bosniya tsohon ɗan jarida ne daga yankin Saarland dake kudu maso yammacin nan Jamus. A shekarar 1981 ya karɓi ragamar shugabancin cibiyar. Aikinsa shi ne kula da kuma gudanar da bincike kan takardun shaida na mutanen da suka kafa ƙungiyoyin musulmi a Jamus tun daga shekarar 1739. Daga baya an ɗora masa nauyin gudanar da bincike game da tattaunawa tsakanin musulmai da kiristoci. A hawa na ɗaya a ginin ofishinsa an rataya kofin wata takarda da sarkin Prussia Friedrich ya rubuta a shekara ta 1740 dake cewa.

“Dukkan addinai ɗaya ne kuma duka suna da kyau. Idan mabiya dukkan waɗannan addinan suka zama mutane na gari to ana iya gina masallatai da coci-coci da sauran wauraren ibada ba da wata matsala ba.”

A wasu ɗakuna dake gaba a cikin wani akwati na katako, Salim Abdullah ya ɗauko wasu tsofaffain littattafai masu bangon fata. Daga ganin waɗannan littattafan ka san an buga su tun wasu ɗaruruwan shekaru da suka wuce.

“A karon farko an tarjama Al-Qur´ani mai tsarki a cikin harshen Latin. Wannan ɗin shi ne bugun farko haɗe da gabatarwa ta Philipp Melanchthon masanin falsafa kuma malamin addini da kuma Martin Luther. An yi masa adana mai kyau.”

Baya ga kayaki na tarihi akwai kuma bayanai da aka tara tun a shekarun 1960 da 1970 lokacin da baƙi ´yan ƙwadago daga ƙasashen Musulmai suka fara kakkafa ƙungiyoyin addinai a yankin Ruhr da kuma yadda Jamusawa suka karɓi baƙwancin sababbin maƙwabtan na su wato Musulmai.

Ban da haka ana gudanar da bincike kan wasu abubuwa na tarihi da ba a san da su sosai ba. Alal misali bincike kan Musulmi ´yan asalin Roma a zamanin mulkin ´yan Nazi Hitler. Bayan binciken farko kan kisan ƙare dangi da aka yi musu a sansanonin gwale gwale, an kuma gano wasu abubuwa sabbi wato adawar da Musulmai suka nuna da mulkin ´yan Nazi.

“A dangane da haka na tuntuɓi majalisar tsakiya ta Sinti da Roma dake birnin Heidelberg. Sun tabbatar min da wannan labari. To amma sun ƙara min da wani bayani daban da cewa duniya ba ta san ainihin abubuwan da suka faru a baya ba wato musulmai sun tayarwa da ´yan Nazi ƙayar baya. Sun nuna adawa da abubuwan da suka wakana a wancan lokaci.”

A cikin shekarar 1927 aka kafa cibiyar tara bayanai da adana kayan tarihi a birnin Berlin da nufin ciyar da tuntuɓar juna tsakanin addainai daban daban gaba. Har yanzu kuwa ta na bin wannan manufa. A majalisar zartaswar akwai wakilan Kiristoci da Yahudawa, wato kamar masanin addinin Kirista na majami´ar Evangelika Hartmut Dreier:

“Abin da muka sa a gaba shi ne mu tabbatar da ɗorewar wannan majalisa wadda ke kula da batutuwan da suka shafi tuntuɓar juna tsakanin mabiya addinai daban daban. Wannan shi ne abin da ya sa cibiyar tara bayanan ta Islama ta yi fice. Ya kuma zama wajibi masu hulɗa da cibiyar tara bayanan sun gane burin da aka sa gaba wato ci-gaba da tuntuɓar juna don kyautata zamantakewa tsakanin mabiya addinan dake a wannan ƙasa. A saboda da haka wanda ya kafa wannan cibiyar a shekarar 1927 Mohammed Nafi Jelebi ɗan ƙasar Syria ya ce ya zama wajibi a ci-gaba da gudanar da tattaunawa da juna sannan kuma a shigar da dukkan waɗanda abin ya shafa a zauren tarukan da ake yi.”

Shekaru 15 bayan kafa cibiyar wato jim kaɗan gabanin ɓarkewar yaƙin duniya na biyu ƙungiyar Musulman duniya ta karɓi ragamar cibiyar. A ƙarshen yaƙin da yawa daga cikin kayakin tarihi sun warwatsu har zuwa farkon shekarun 1970 lokacin da wani jami´in diplomasiya ya tambayi Salim Abdullah wanda a lokacin yake aikin jarida a Saarland, ko zai iya kula da aikin adana kayakin tarihin.

“Ina samun takardu iri daban daban da suka haɗa da na amsoshin tambayoyi da rasitai da sauran takardun shaida na karo-karon wanda aka biya tun bayan kafa wannan cibiyar tara bayanai a Jamus.“

Yanzu dai wannan cibiyar na matsayin wani wurin neman bayanai da kayakin tarihi musamman ga hukumomi da sauran masu bincike kan tarihin Musulmai da addinin na Musulunci a nan Jamus.