1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080908 Goethe-Institut Afrika

Bloch, WernerSeptember 18, 2008

Cibiyar ta yaɗa al´adun Jamus ta fara faɗaɗa ayyukanta a Afirka.

https://p.dw.com/p/FKOr
Shugaban Goethe-Institut Klaus-Dieter LehmannHoto: picture-alliance/ dpa

Jama´a barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da shafi al´adu, addinai da zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban a wannan duniya ta mu.


An daɗe ana yiwa Afirka kallon wata nahiya da aka manta da ita. To amma hakan ya canza. Yayin da China a diplomasiyance ta tabbatarwa kanta wani kaso na albarkatun ma´adanai da Allah Ya bawa wannan nahiya sakamakon dogon barci da ƙasashen suka yi a wannan fanni. To sai dai yanzu Jamus ta buɗe sabon dangantaka ta al´adu a wannan nahiya, inda cibiyar yaɗa al´adu ta Goethe Institut ta fara faɗaɗa ayyukanta a Afirka. A baya-bayan nan cibiyar ta buɗe wani sabon ofishinta a Tanzania kuma ta na shirin buɗe wasu sabbi a Sudan da Angola ƙarƙashin wani shiri da mai taken mayar da hankali kan Afirka bayan shekaru da dama ta na rufe cibiyoyinta a wannan nahiya. Hakan ya samu sakamakon ƙarin kasafi da take samu daga gwamnatin tarayya.


Yayin bukin buɗe sabuwar cibiyar yaɗa al´adun Jamus kenan wato Goethe-Institut a Dares-Salam babban birnin ƙasar Tanzania. Makiɗan ƙasar da takwarorinsu daga Jamus suka yi wasan kiɗa ƙarƙashin gayyatar cibiyar ta Goethe-Institut. An yi wannan buki ne a wani lambu na ganyaye wanda wani Bajamushe ya kafa a shekarar 1893. A jawabinsa na buɗe sabuwar cibiyar, shugaban Goethe-Institut Klaus-Dieter Lehmann cewa ya yi.


“Mun yi wa Afirka riƙon sakainar kashi. Amma ka da mu manta ana ganin mutuncin Jamusawa a wannan nahiya. Hakan wata dama ce da ya kamata mu yi amfani da ita domin taka kyakkyawar rawa wajen ci-gaban nahiyar. Manufarmu shi ne aiki a matsayin abokan hulɗa amma ba ´yan mishan ba. Za a cimma nasara idan dukkan sassan biyu suka so yin haka.”


Shi dai Klaus Dieter Lehmann wanda aka ba shi shugabancin cibiyar a ranar ɗaya ga watan Afrilu, ya fara wannan aiki ne a wani lokaci da cibiyar ke samun haɓaka bayan shekaru da yawa koma-baya. Yanzu dai cibiyar ta sake buɗe ofishinta a Tanzaniya bayan rufe shi da ta yi shekaru 10 da suka wuce sakamakon matakan tsimi da tsohon ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ɗauka. An jiyo ministan harkokin wajen Tembe wanda shi ma ya halarcin bukin buɗe sabuwar cibiyar ta Goethe-Institut yana cewa.


“Babban aikin da cibiyar ta sa a gaba a birnin Dares Salam shi ne haɓaka koyon harshen Jamusanci da ƙarfafa musayar al´adu tsakanin Tanzania da Jamus. Za ta taka rawa wajen inganta harkar ba da ilimi da masaniya game da Jamus ta hanyar ba da bayanai game da fasahohi da al´adu da zamantakewa da kuma siyasar Jamus.”


Yankin gabashin Afirka dai ya taɓa zama ƙarƙashin ikon Jamus tsawon shekaru 34 inda aka yi murƙushe masu ta da ƙayar baya. To sai dai abin mamaki duk da haka ana ganin martabar ƙasar ta Jamus a Tanzania. Da yawa daga cikin matasan Tanzania suna sha´awar neman ƙarin ilimin jami´a a Jamus saboda haka suke koyan harshen Jamusanci da kuma al´adun Jamusawa a cibiyar ta Goethe-Institut kamar yadda shugabar cibiyar a ƙasashen Afirka 47 Katharina von Ruckteschell ta nunar.


“Na yi imani cewa manufofin Jamus dangane da al´adu a Afirka da ma a wasu ƙasashen na da kyau domin suna ƙoƙarin nuna irin wuraren tarihi da na al´adu da muke da su. Hakazalika suna mayar da hankali kan buƙatun mu gaba ɗaya musamman wajen musayar al´adu. Ba masu fasaharmu muke turowa Afirka domin su baje kolin ayyukansu ba, a´a muna duba irin ƙwararrun masu fasaha dake a nahiyar ta Afirka da kuma haɗin kan da za a samu tsakaninsu da takwarorinsu na Jamus.”


Tarayyar Nijeriya ma na daga cikin ƙasashen da Goethe-Institut ta fara faɗaɗa ayyukanta, inda yanzu haka ta buɗe reshenta a birnin Kano. Tun a shekarar 1962 Goethe Institut take a Nijeriya amma a birinin Legas. Daraktan cibiyar a Legas Armin Schneider ya nuna farin cikinsa da wannan mataki da cibiyar ta ɗauka wanda ya ce haka zai ƙarfafa haɗin kai da musayar al´adu tsakaninsu da sauran al´ummomin Nijeriya.


“A tsawon shekaru 46 a Nijeriya mun fi gudanar da ayyukanmu ne a kudancin ƙasar, amma tun daga bara mun fara tafiyar da wasu aikace-aikace a Kano, tare da haɗin guiwa da cibiyar tarihi da yaɗa al´adu a jihar Kano. Kuma yanzu muna kan buɗe reshenmu a Kano, inda tun a cikin Satumba wakilinmu ya ke can ya na aikin share fage.”


Daraktan na Goethe Institut a Legas ya ce a halin yanzu suna aikin musayar al´adu ne da hukumomin Kano da sauran ƙungiyoyin al´adu na wannan jiha amma za su buɗe sashen koyar da harshen Jamusanci da zarar bukatar haka ta taso.


“A ziyarar da na kai Kano na gana da wakilai cibiyoyin al´adu na Birtaniya da Faransa da wasu ƙungiyoyin ´yan Nijeriya kamar ƙungiyar masu shirya fina finai. Na kuma ziyarci jami´o´i shi yasa ina ganin za mu samu dukkan goyon bayan da muke buƙata a Kano.”


Yanzu dai ana iya cewa Allah Ya ɗigawa garin wannan cibiyar ta yaɗa al´adun Jamus nono, domin a bana ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta tanadar mata kudi sama da euro miliyan 700 a kasafin kuɗi na shekara mai zuwa. A dangane da goyon bayan da take samu daga wannan gwamnati, a farkon mako shugabar gwamnati Angela Merkel ta kai ziyara a hedkwatar cibiyar dake birnin Munich inda ta ƙarfafa muhimiyar rawar da Goethe Institut ɗin ke takawa a wannan mara ta haɗakar manufofi da kyautata fahimtar juna tsakanin al´adu.


“Yanzu muna rayuwa ne a cikin wani zamani na yawaitar amfani da yanar gizo, inda kai tsaye mutum ke iya samun dukkan bayanan da ya ke buƙata. To amma duk da haka ba mu da ƙarfin gane haɗakar dake tsakanin bayanai da kuma fahimtar su.”


Ziyarar ta Merkel ta buɗe sabon babi ga cibiyar wadda, wadda bayan komabaya da ta fuskanta a cikin shekarun 1990 yanzu take ƙara samun ci-gaba. Yanzu ana iya cewa manufar Jamus da suka shafi yaɗa al´adu ta komo matsayinta kamar yadda Willy Brandt ya ajiye ta a shekarun 1970 wato ta mataki na uku na manufofin Jamus da suka shafi ƙasashen ƙetare.