1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba akan gubar sinadarin Lead a Zamfara

June 19, 2010

An fara samun nasarar shawo kan gubar sinadarin Lead a jihar Zamfara dake arewacin Nijeriya

https://p.dw.com/p/NxU8
Wasu ƙananan yara dake samun kulawa ta lafiya.Hoto: Monika Hoegen

Hukumomin lafiya a Nijeriya sun ce an fara samun nasarar shawo kan sindarin Lead a Jihar Zamfara wadda ta yi sanadiyar hallaka yara kimanin 163 da kuma haddasa rashin lafiya ga mutane fiye da 300. Dr Sani Gwarzo ɗaya daga cikin likitocin dake jagorantar shirin kula da lafiyar mutanen da suka kamu, yace ya zuwa yanzu an sami nasara wajen rage yawan marasa lafiyar da kuma macecen da aka yi.

Dr Sani Gwarzo yace tun da aka fara wannan kai dauki, ba'a kuma samu rasuwar wani yaro ba. Haka zalika yace marasa lafiya ma sun fara raguwa saboda matakan da aka dauka na rage cudanyar mutane da wannan sinadari na Lead. Mutanen dai sun kamu da gubar sinadarin ce sakamakon aikin sarrafa Guza wadda suke fidda zinariya daga cikinta. A yanzu dai an fitar da dukkan Injinan da ake sarrafa wannan zinariya zuwa wajen gari yayin da a waje guda ake cigaba da kankare ƙasar da ke gidaje da kuma mayar da gurbinta da wata ƙasar mai kyau.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita Halima Balaraba Abbas