1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba da shariár Saddam Hussaini

March 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5I

A ranar lahadin nan ake cigaba da shariár tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussaini tare da mukarraban sa su bakwai a game da tuhumar da ake musu ta kisan mutane 148 a kauyen Dujail a zamanin mulkin sa. Bayan kammala jin baási daga wadanda ake zargi kotun za kuma ta saurari bayanai daga shaidu. Hukumar kare hakkin bil Adama ta majalisar dinkin duniya ta soki lamirin kotun dake shariár Saddam inda ta baiyana cewa kamata ya yi a gurfanar da shi ne ga kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya don samun adalci. Hukumar ta ce duk da cewa duniya ta amince da yiwa Saddam shariá a kan laifukan da ya aikata a zamanin mulkin sa, akwai bukatar gudanar da shariár bisa gaskiya da adalci. Lauyoyin dake kare Saddam sun kudiri aniyar kalubalantar kotun ta kasar Iraqi wadda suka ce ba halastacciya ba ce. Babban alkalin kotun Rauf Rasheed Abdel Rahman Bakurde ne wanda ya fito daga yankin da ake zargin Saddam da halaka wasu alumar yankin ta hanyar isaka mai guba a tsakanin shekarun 1980 zuwa 1988.