1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban arangama tsakanin Jami'an tsaro da masu adawa da gwamnati a Thailand

May 14, 2010

Masu adawar Red shirts na cigaba da ƙone-ƙonen motocin jami'an tsaro a birnin Bangkok

https://p.dw.com/p/NNGL
Hoto: AP

Sojoji a Bangkok, babban birnin ƙasar Thailand, sun buɗe wuta akan masu zanga zangar nuna adawa da gwamnati, a lokacin farmakin da suka kai domin killace wani yanki, inda masu zanga-zangar suka kafa sansaninsu.

An kashe wani mai zanga-zanga guda ɗaya,  sannan wani sojan da ya bijirewa gwamnati, Manjo Janar Khattiya Sawadispol, wanda yake baiwa masu zanga-zangar shawara kan yadda ake ɗaukar matakan tsaro, yana daga cikin waɗanda suka jikkata. Sai dai gwamnatin ƙasar ta sanar da gudanar da bincike kamar yadda kakakinta Panitan Wattanayagorn ya sanar, " za a gudanar da bincike a dukkan hatsarin da suka auku. Abun takaici ne yadda wannan rikici ke cigaba da ruruwa. Bamu da wani tsari da ke bawa jami'an tsaronmu damar ɗaukar wannan mataki. Muna gudanar da dukkan lamuranmu ne bisa ga tsarin kare hakkin jama'a da ƙasa".

Mawallafiyya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu