1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban sharár Saddam Hussaini

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv31

A yau ake cigaba da shariár tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussaini bayan tsaiko na makwanni uku inda zai fuskanci wasu zargi na kisan ƙare dangi. Kotun ta baiyana cewa a karon farko Saddam tare da mukarraban sa su shida za su fuskanci tuhuma a game da kisan kiyashi da aka yiwa yan ƙabilar kurdawa da ya hallaka mutane 180,000 a zamanin mulkin sa. Tuni dai Saddam tare da wasu muƙarraban na sa, su bakwai suke fuskantar shariá a dangane da kisan mutane 140 mabiya ɗarikar shiá dake garin Dujail a sakamakon yunkurin hallaka shi a shekarar 1982. Masu gabatar da ƙara sun ce tsaikon da aka samu na mawanni uku, an yi ne da nufin baiwa alƙalai, damar tsara laifukan da ake tuhumar Saddam ɗin da aikatawa da kuma sake nazarin shaidu domin kaiwa ga mataki na gaba na shariár. Babban mai gabatar da ƙarar Jaáfar al-Musawi yace Saddam ya kammala bada baási abin da ya rage shi ne yi masa tambayoyi wanda lauyoyi za su a yau. To amma lauyoyin Saddam sun ce Saddam bai gama bada bayanan sa ba, domin kuwa yana da sauran abubuwan da zai faɗa. Mai gabatar da karar yace akwai bayanai da aka samu waɗanda ke danganta Saddam da laifuka da ake tuhumar sa a kan su.