1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban zanga zanga a ƙasar Hungary

September 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuiM

Dubban masu zanga zanga a ƙasar Hungary, sun lashi takobin cigaba da ƙudirin su na mastin lamba ga P/M ƙasar har sai ya yi murabus. Dubban masu adawa da gwamnatin sun cigaba da zanga zangar a birnin Budapest a jiya lahadi wanda suka shafe tsawon mako guda suna gudanarwa, ko da yake an sami raguwar jamaár daga 40,000 waɗanda suka yi dandazo a wajen ofishin majalisar dokoki. Mutane waɗanda yawan su ya kama daga 5,000 zuwa 10,000 ne suka hallara a dandalin Kossuth domin yin kira ga P/M Ferenc Gyurcsany ya sauka daga muƙamin sa. Zanga zangar ta samo asali ne bayan da aka tseguntawa kafofin yada labarai wani kaset inda P/M ya amsa cewa jamíyar sa ta Socialist ta shirga karya domin samun nasarar lashe zabe a cikin watan Aprilu. P/M dai yace ba zai sauka daga mukamin sa ba, yana mai cewa zai cigaba da aiwatar da manufofin sa na karin haraji da kuma rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa domin cike giɓin kasafin kuɗi, matakan da masu zanga zangar ke nuna adawa da su.