1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban zanga zanga a Beirut

December 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuYx

Kungiyoyin yan adawa a karkashin jagorancin Hizbollahi na kasar Lebanon,sun sanar dacewa a shirye suke na fadada kamfaign dinsu ,domin hambare gwamnatin da sukace na kasashen yammci ,tare da kira da a gudanar da sabuwar zanga zanga na kasa baki daya.

Yau ne aka shiga rana ta shida,da dubban yan adawan ke gudanar da wannan bore a kusa da headquatan gwamnatin kasar,wanda ya dakatar da harkokin gudanarwan bankuna da dana kasuwanci a birnin Beirut.Yan adawan dai sun lashi takobin cigaba da gudanar da wannan bire,har sai prime minista Fouad Siniora,yayi murabus daga mukaminsa.Tuni dai Premien Lebanon din yayi kira ga yan adawan dasu dakatar da wannan bore akan tituna,domin komawa teburin tattaunawa,inda yace babu wanda zai tilasta masa ajiye mukaminsa.