1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikanta yarjejeniyar bada mai tsakanin Koriya ta kudu data Arewa

July 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuF9

Koriya ta kudu ta aike da jirgi na biyar kuma na karshe dake dauke da zuwa kasar koriya ta Arewa,wanda ke zama mataki na farko adangane da batun watsi da makaminta na Nuclear.Jirgin ruwan wanda ke dauke da Ton na man petur dubu 22 da 600,da safiyar yau yabar tashar jiragen ruwa dake Ulsan,akan hanyarsa zuwa Jeong Gil-Ju dake koriya ta arewa.

A karkashin matakin farko na yarjejeniyar da kasashe 6 masu tattauna rikicin nuclearn koriya ta arewan suka cimmawa a watan febrairu,kasar ta koriya ta arewa dake fama da karancin man petur,zata karbi Ton dubu 50 na mai,a madadin rufe cibiyar sarrafa Atom dinta dake Yongbyon,a gaban masu binciken harkokin nuclear na mdd.A ranar 12 ga wannan wata na yuli nedai koriya ta kudu da kaddamar da wannan alkawari da aikewa makwabciyar tata ton dubu 6,200 na man petur.