1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikar shekaru 60 da kwaco sansanin Buchenwald

April 11, 2005

A ranar 11 ga watan afrilun shekarar 1945 ne aka kwaco sansanin gwale-gwale na Buchenwald daga 'yan Nazi

https://p.dw.com/p/BvcT
Sansanin gwale-gwale na Buchenwald
Sansanin gwale-gwale na BuchenwaldHoto: AP

Sansanin gwale-gwalen na Buchenwald na daya daga cikin manyan sansanonin da ‚yan nazi suka tanadar domin azabtar da fursinoni, inda a tsakanin 1937 zuwa 1945 aka tsare fursinoni kusan dubu 250 daga kasashe 30, kuma fursinoni dubu 56 daga cikinsu suka yi asarar rayukansu.

Wannan wani bangare ne na wakar da fursinonin su kan rera a duk lokacin da suka yi jerin gwano zuwa bakin ayyukansu a gidan yari, wacce kuma akan shigar da ita a duk lokacin da ake bikin tunawa da mutanen da ta’asar ‚yan nazinhitler ta rutsa dasu a wannan sansani na Buchenwald. Wani bafaranschen da ake kira Bertrand Herz yana da shekaru 15 na haifuwa lokacin da yayi asarar iyayensa a sansanin gwale-gwalen na Buchenwald, kuma yau shekaru 60 bayan haka ya gabatar da kira ga matasa da su dauki wannan sansanin tamkar wa’azi garesu. Kamar yadda muka yi bayani can baya fursinoni dubu 56 suka yi asarar rayukansu sakamakon yunwa da radadin sanyi da kuma azabtarwa a hannun baraden Hitler na SS. Wadannan fursinoni sun hada da Yahudawa da ‚yan kabilun Sinti da Roma da fursinonin siyasa da kuma fursinonin yaki daga Tarayyar Soviet. Daga cikin mutane dubu 21 da suka tsira daga sansanin na Buchenwald, wasu 500 sun halarci dandalin bikin a Weimar. A cikin jawabinsa na marhabin da mahalarta bikin shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya fara ne da mika sakon gaisuwarsa ga wadannan tsaffin fursinoni, wadanda ba zato ba tsammani suka rika yi masa tafi da guda.

Schröder ya ce babban alhakin da ya rayata wuyanmu a yanzun shi ne mu yi bakin kokarinmu wajen kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin dukkan jinsunan mutane dake nan kasar da kuma sauran kasashe na nahiyar Turai. Ya ce ko da yake ba za’a iya warkar da wannan tabo na tarihi ba, amma akalla ana iya koyan darasi daga gare shi. Ana iya koyan darasi daga wannan abin kunyar da ya rutsa da al’umar Jamus. A nasa bangaren shugaban kwamitin Yahudawan jamus Paul Spiegel yayi tsokaci da barazanar da ake dada fuskanta daga masu zazzafan ra’ayi irin na Hitler, lamarin dake kara yin tsamari tun bayan da suka samu wakilci a majalisun jihohin Sachsen da Brandenburg. Ya ce wannan mummunan ci gaba wajibi ne a nemi kwararan hanyoyin dakatar da shi tun kafi ya zama gagara-badau. Domin kuwa ainifin babban burin wadannan masu zazzafan ra’ayi irin na Hitler shi ne ganin sun zama wani cikakken bangaren da za a rika damawa da su a siyasar Jamus nan gaba.