1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikar wa'adin janye dakarun Amirka daga Iraƙi

August 31, 2010

A yau Talata ce wa'adin janye sojojin Amirka da ke Iraƙi ya cika bayan yaƙi na tsawon shekaru 7

https://p.dw.com/p/OzxN
Hoto: AP

Bayan fiye da shekaru bakwai da Amirka ta jagoranci mamayar ƙasar Iraƙi, a yau Talata ce wa'adin janye dakarun ta dake fagen fama ya cika. Shugaban Amirka Barak Obama ya sanar da cewar kamata ya yi ɗaukacin dakarun da ke fagen yaƙin su janye. Aƙalla sojojin Amirka dubu 50 ne za su rage a ƙasar domin bayar da horo ga sojojin Iraƙi. Nan da ƙarshen shekara ta 2011 kuma dukkan rukunan sojin Amirka za su fice daga Iraƙi.

A jiya Litinin ne mataimakin shugaban Amirka Joe Biden ya sauka ƙasar ta Iraƙi domin baiwa hukumomin ƙasar tabbacin cewar janye dakarun Amirka daga fagen fama, baya nufin Amirka ta yi watsi da su bane. An kuma tsara cewar Biden zai gudanar da tattaunawa tare da shugabannin ƙasar ta Iraƙi, waɗanda suka gaza cimma daidaito game da kafa sabuwar gwamnati kimanin watanni shidda kenan bayan gudanar da zaɓukan majalisun dokoki a ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu