1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikin wani rahoto da shugaban hukumar kula da yan gudun hijira ta ...

December 12, 2003
https://p.dw.com/p/Bvn9
majalisar dikin duniya da kuma wata kungiyar bada agaji mai zaman kanta ta Japan suka fitar,sun baiyana cewa kasar Africa ta kudu na zaman daya daga cikin kasashen Afruka da halin yanzu ke karbar bakuncin yan gudun hijira da akoda yaushe ke tururuwa zuwa wanan kasa ta kudancin Afruka daga sasa dabam dabam na nahiyar Africa. Ana dai baiyana cewa kashi kimanin kashi daya cikin uku na yan gudun hijira da kuma masu neman mafakar siyasa 90,000 dake zaune a kasar Africa ta kudu nada ilimin zamani.kashi biyu cikin uku na yan gudun hijirar dake zaune a Africa ta kudu nada shaidun kamala ilimin sakandare,ko kuma wani abu da yayi kama da haka,yayin kuma da wasun su kuma ke da sana'oi na hanu kafin issa kasar ta Africa ta kudu. To sai dai kuma da zarar irin wadanan yan gudun hijira da suka fito daga wasu kasahe na Africa sun issa kasar ta Africa,sai alamura su chanza salo baki daya.

Yayin da kashi uku daga cikin dari na yan gudun hijira suka zamanto basu da wata sana'ar yi daga kasahen da suka yi kaura,hata ma a Afruka ta kudun bata sake zani ba.Kusan rabin mutanen dake gudun hijira a Africa ta kudu kann sami sukunin tura yayan su zuwa makaranta.

Yan gudun hijira dai dake zaune a Africa ta kudu nada yancin baiwa yayan su ilimin Primary da kuma cin gajiyar matakan kula da lafiya na gaugawa,kamar dai yadda yan Africa ta kudu ke samun irin wanan dama,to sai dai kuma a wasu lokutan basa samun irin wanan dama a sabili da matsaloli na rashin abin hanu.

A wani bincike da aka shafe shekaru biyu ana yi game da yan gudun hijirar dake zaune a kasar Africa ta kudu,yayin da aka gudanar da gwaji kann yan gudun hijira 1,500 dake zaune a birnin Johanesburg,Cape Town,Duban,da kuma Pretoria,an gano cewa wadanan yan gudun hijira sun fito ne daga kasahen Angola,jamhuriyar democradiyar Congo,Somalia,Congo.Brazzavill,Burundi,Ruwanda Ethiopia,Uganda,Sierra Leone,Sudan,Liberia da kuma kamaru.

Sauran yan gudun hijirar dake zaune a kasar ta Africa ta kudu sun fito ne daga Zimbabwe. Bemma Donkoh wakilin baban Comishinan hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dikin duniya,ya furta cewa wanan shine lokaci na farko da hukumar su ta yi nazari game yadda yan gudun hijirar dake zune a kasar Africa ta kudu ke gudanar da harkokin rayuwar su ta yau da kulum,wanda kuma ta haka ne za'a samar da matakan kare mutuncin su,tare kuma basu taimako. Jami'in dai na hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a Africa ta kudu,ya baiyana cewa da dama daga cikin yan gudun jirar dake da ilimin zamani ko kuma sana'ar hanun,sun nuna aniyar su ta bada tasu gudunmawar wajen cigaban wanan kasa ta kudancin Africa. Bincike ya nuna cewa kashi 44 daga cikin dari na yan gudun hijirar dake zaune a Africa ta kudu kann sami ikon cin abinci ne sau daya a rana,yayin da kashi 21 daga cikin dari kuma ke kokawa da cewa basa iya ciyar da iyalan su. Kusan kashi uku daga cikimn dari na yan gudun hijira dake zaune a Africa ta kudu,dake neman aiyukan yi kann koka da cewa basa samun wanan dama,a sabili matsaloli na rashin issasun takardun izinin zaman kasa,koda dai yake gwamnatin Africa ta kudu na fama da karancin maikata a wasu sasanta na maikatun gwamnati.