1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci a Najeriya

July 9, 2010

Hukumar yaƙi da halarta kuɗin haram ta Najeriya wato EFCC, ta buƙaci Birtaniya ta tiso mata ƙiyar wani jami'i da take nema ruwa a jullo

https://p.dw.com/p/OFb2
Tutar Najeriya

Najeriya ta buƙaci da ƙasar Birtaniya ta tiso mata ƙiyar wani jami'in bankin ƙasar wanda aka kora, bayan sargin yin sama da faɗi. Hukumar EFCC daƙe yaƙi da halarta kuɗin haram, tace ta miƙa buƙatar ga gwamnatin Birtaniya, da ta turo mata Erastus Akinbola tsohon shugaban bakin Interconental, wanda ya pice daga ƙasar jim kaɗan bayan da gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya sanar da korar wasu shugabannin bankuna biyar, waɗanda suka yi kusan dunƙufar da harkar bankuna na ƙasar, inda suka yi ta bada basuka, batare da bin ƙa'ida ba, abinda yasa tattalin arzikin ƙasar ya fara shiga uku. Kakakin hukumar EFCC Mr Femi Baba Femi, ya ce dama kotu ta yankewa Ankinbola hukunci bayan idonsa, kana yace Kotun ta bada izinin rufe ajiyarsa ta kuɗi zunzurutun na Naira miliyan dubu 346. Har sai an yanke hukunci kan laifuka 28 da ake cajinsa a kotu. Tuni dai lawyan wanda ake zargin, yace sun shigar da ƙara a London, domin hana picewa da wanda ake zargin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu