1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci na hana ruwa gudu ga ci gaban Afirka

November 13, 2009

Cin hanci da almundahana matsaloli ne da suka zama ruwan dare a Afirka suke kuma yin cikas ga ci gaban ƙasashen nahiyar

https://p.dw.com/p/KWUw
Jami'ar siyasa kuma alƙali Eva Joly ta FaransaHoto: DW

A wannan makon ma dai jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran Afirka, musamman ma a game da matsalar cin hanci da ta zama ruwan dare a ƙasashen nahiyar. A cikin nata rahoton jaridar Die Tageszeitung ta ba da la'akari ne da yadda manyan kamfanoni na ƙasa da ƙasa ke da hannu dumu-dumu a matsalar cin hanci da ba da toshiyar baki a ƙasashe masu tasowa. Jaridar tayi hira da wata jami'ar siyasa kuma alƙali a ƙasar Faransa Eva Joly akan wannan matsala da kuma yadda za a tinkare ta a daidai wannan lokacin da ake fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙin duniya. Jaridar dai ta ambaci jami'ar siyasar tana mai cewar:

"Yaƙi da cin hanci abu ne mai muhimmanci matuƙa da aniya, saboda matsala ce dake hana ruwa gudu wajen ci gaba ƙasa saboda tana toshe dukkannin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da ake buƙata don gina ƙasa. Kuma ma ba cin hanci ne kawai matsalar da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta ba, abin ya haɗa da dukkan hada-hada ta kuɗi ta hanyar da ba ta dace ba. Misali toshiyar baki da manyan kamfanoni ke bayarwa yawansa bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da irin ƙazamar ribar da zasu samu. Misali yawa-yawancin waɗannan kamfanoni ko haraji ma ba sa biya a ƙasashen Afirka kuma ba wani mai saka ayar tambaya game da haka."

Tschad Ölförderung Arbeiter Doba Ölfelder
Dangantakar Afirka da ChinaHoto: AP

Ƙasashen yammaci dai sun daɗe suna bayyana damuwarsu a game da yadda China ke ƙoƙarin yaɗa angizonta a nahiyar Afirka, a yayinda a nasu ɓangaren ƙasashen Turai da Amirka ke daɗa zama 'yan rakiya a wannan nahiya. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"A haƙiƙa ba kawai dangantakar tattalin arziƙi ce kawai ta haɗa China da Afirka ba. Kazalika dukkan sassan biyu na ɗariɗari da manufofin ƙasashen yammaci, waɗanda ke ƙyamar mulke-mulke na kama karya. Bugu da ƙari kuma ba gwamnatin China ce kaɗai ke zuba jari a Afirka ba, har ma da wasu kamfanonin ƙasar masu zaman kansu, waɗanda ke gogayya a na ƙasashen yammaci."

Italien Cap Anamur Flüchtlinge Sudan Sudanesische Einwanderer Flash Galerie
An samu raguwar kashi 90 cikin ɗari na 'yan gudun hijirar Afirka a TuraiHoto: AP

A daidai lokacin da ake bikin rushewar katangar Berlin da ta raba ƙasashen yammaci da na gabacin turai a zamanin yaƙin cacar baka, a yanzu shingen ya kankama ne tsakanin Turai da Afirka, inda aka samu raguwar kashi 90% na yawan 'yan gudun hijirar Afirkan dake malalowa zuwa Turai, in ji jaridar Die Tageszeitung, wadda ta ce an samu wannan ci gaba ne sakamakon matakan Libiya na mayar da 'yan gudun hijirar ƙasashensu tare da taimakon ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu