1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin mutane a Bangui

Usman Shehu UsmanAugust 12, 2015

MDD ta kaddamar da bincike, bisa rahoton da ya bayyana cewa sojojinta da ke aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun hallaka woni saurayi da iyayensa daga bisani suka yi wa wata yarinya fyade.

https://p.dw.com/p/1GDly
Zentralafrikanische Republik Bangui Minusca UN-Truppen
Hoto: picture-alliance/AA

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta ce lamarin ya faru ne a makwan jiya bayan wata takadda da aka samu tsakanin sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashen Kamaru da na Ruwanda da mazauna birnin Bangui. Dama tuni MDD ke binciken batun yin latata da yara wanda aka zargi sojan kasar Faransa da aikatawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A yanzu haka MDD na da sojoji kimanin 10.000 da ke aikin raba fada tsaklanin mayakan kiristoci da na musulmai a kasar.