1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makamai tsakanin Amirka da Saudiyya

September 14, 2010

Amirka za ta samar da aikin yi ga 'yan kasar ta hanyar sayarwa Saudiyya makamai

https://p.dw.com/p/PBVl
Ginin ma'aikatar tsaron Amirka ta PentagonHoto: AP

Gwamnatin Amirka a karkashin jagorancin shugaban kasar Barak Obama ta sanar da shirin sayarwa kasar Saudiyya da makaman da suka kai na kudi dalar Amirka miliyan dubu 60, wato kwatankwacin Euro miliyan dubu 47. Aiwatar da wannan yarjejeniyar dai za ta sa hakan ta zama kwangilar sayar da makamai mafi girma a tarihi. Jami'an gwamnatin Amirka su ka ce yarjejeniyar za ta taimaka gaya wajen samar da dubbannin gurabun aikin yi ga 'yan kasar ta, yarjejeniyar da kuma a karkashin ta Saudiyyar za ta sayi jiragen saman yaki har guda 15.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ya ce nan da kwanaki masu zuwa ne majalisar dokokin kasar ta Amirka za ta sami bayani a hukumance game da yarjejeniyar, wadda kasar ta dade tana jiran ganin an kulla ta. Hakanan Amirkar, tana tattaunawa da kasar Saudiyya domin sake fasalin tsarin na'urorin kakkabe makaman linzamin ta, yadda za su dace da na zamani.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala