1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin Makaman KUngiyar Tarayyar Turai

November 17, 2004

Kasashen KTT, musamman Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya da Sweden, suna daga cikin gaggan kasashen da suka fi cinikin makamai a duniya

https://p.dw.com/p/BveZ

Rahoton, wanda ga alamu akasarin wakilan majalisar zasu yi na’am da shi, Raul Romeva Rueda daga kasar Spain ne ummal’aba’isin gabatar da shi, domin yin tsokaci da yadda mahukuntan kasashen kungiyar tarayyar turai ke fatali da ka’idojin cinikin makaman da aka shimfida tun a shekarar 1998. A karkashin wadannan ka’idojin an yi bayani filla-filla a game da ire-iren makaman da za a iya fitar da su zuwa ketare. Misali an hana fitar da makaman zuwa kasashen dake amfani da su domin take hakkin dan-Adam, ko kuma zuwa yankunan da ake fama da rikici ko fuskantar barazanar billar rikici a cikinsu. Kazalika ba a yarda da a fitar da makaman zuwa kasashen da cinikin wadannan makamai ke dada jefa al’ummominsu cikin mawuyacin hali na talauci da matsaloli na rayuwa ba. To sai dai kuma ba a wajabta biyayya ga ka’idojin ba, illa kawai kiran nuna halin sanin ya kamata akan manufa, duk kuwa da cewar kimanin kashi 80% na makaman ana cinikinsu ne a kasashen dake wajen nahiyar Turai. Romeva Rueda yayi suka da kakkausan harshe akan fitar da makaman da ake yi zuwa kasashen dake amfani dasu domin take hakkin dan-Adam. Sai ya kara da bayanin cewar:

"Wasu daga cikin makaman ana amfani da su ne wajen azabtar da fursinoni, ko kuma wata fasaha ta wanzar da hukuncin kisa, ko kuma wasu na’urori na gallazawa da keta haddin dan-Adam. Misali akan fitar da ire-iren kulaken nan masu wutar lantarki, wadanda mahukunta na ‚yan sanda ke amfani dasu domin tilasta wa fursuna yin na’am da laifin da ake zarginsa da aikatawa."

Wakilan majalisar ta Turai kazalika har yau suna adawa da shawarar dage takunkumin haramcin sayarwa da kasar China makamai. Kasashen Jamus da Faransa ne suka ba da shawarar dage takunkumin, wanda aka kakaba wa China a shekarar 1989. Bisa ga ra’ayin wakilan majalisar tilas ne a samu canjin manufofin China daga tushensu kafin a tsayar da wata shawara ta sake kama harkar cinikin makamai da ita. Kasar har yau tana ci gaba da take hakkin dan-Adam. Bugu da kari kuma akwai barazanar rikici tsakaninta da Taiwan. A saboda haka lokaci bai yi ba da za a soke wannan takunkumi akanta.