1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Clinton ta kai ziyara a Pakistan

HaliJuly 19, 2010

Sakatariyar harkokin wajen ta ce ƙasarta za ta taimaka wa Pakistan

https://p.dw.com/p/OP2j
Hillary Clinton tare da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari.Hoto: AP

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton ta isa ƙasar Pakistan inda ta shiga tattaunawa tare da manyan jami'ai a matsayin yanki na rangadin diplomasiya irinsa na farko da take yi a wannan yanki. Clinton ta ba da sanarwar ba da taimakon dala miliyan dubu 7 da miliyan ɗari biyar domin samar da ruwa da makamashi da kuma asibitoci a wannan ƙasa.

Wannan shiri ya haɗa ne da gina madatsun ruwa guda biyu da sabbin asibitoci da kuma sabon shirin samar da ruwan sha. Bayan ganawarta da shugabannin siyasar Pakistan, Clinton ta faɗa wa manema labarai cewa waɗannan ayyukan alamu ne da ke nuni da cewa ba ma akan aikin tsaron ƙasar nan ne kaɗai Amirka ke mai hankali ba. Ta ce; "Mun ƙuduri niyyar ƙarfafa dangantakarmu da Pakistan ba ma a fannin aikin tsaro kaɗai ba. Amma da nufin kare al'uma. Muna buƙatar samar da ci gaban tattalin arziƙi da kuma ƙarfafa rassan gwamnati a baya ga samar da ababan jin daɗin rayuwa.

A jiya Lahadi ne Clinton ta isa ƙasar ta Pakistan bayan da aka rattaba hannu kan yarjejrniyar kasuwanci tsakanin Afganistan da Pakistan da ake sa ran za ta kawo sauƙin shige da fice tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Zainab Mohammed Abubakar