1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cocin Katolika a Kwango ta yi kira ga ƙaurace wa zaɓen ƙasar.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupT

Shugabannin cocin Katolika a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango sun yi kira ga masu ka da ƙuri’a da su ƙaurace wa zaɓen da aka shirya yi a ranar lahadi mai zuwa, idan kafin lokacin, ba a warware batun zargin da ake yi wa mahukuntan ƙasar na yunƙurin tabka maguɗi a zaben ba. Wata sanarwar da aka karanta wa mabiya ɗariƙar katolikan a taron ibada a duk faɗin ƙasar yau ta ce ruɗamin da ake ta ƙara samu kan yawan waɗanda aka yi rajistansu su ka da ƙuri’u da kuma ƙarin yawan takardun ƙuri’un da aka buga, na nuna cewa akwai wani shiri a ɓoye na tabka maguɗi a zaɓen na ranar 30 ga wannan watan. Sabili da hakan ne dai cocin ke kiran mabiyansa da su ƙaurace wa zaɓen, idan ba a warware waɗannan matsalolin ba, inji sanarwar.

Tun ran juma’ar da ta wuce ne dai shugabannin cocin suka ce har ila yau ba a cika duk ƙa’idojin da suka dace wajen gudanad da zaɓen cikin adalci da lumana ba. Idan ko ba a yi gyara ba, to cocin ba za ta amincce da sakamakon ba.

Amma hukumar zaɓen ƙasar Kwangon, wadda tare da goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ke shirya zaɓen, ta yi watsi da sukar da cocin ke yi mata. Kuma ta ce za gudanar da zaɓen kamar yadda aka shirya.